Mark Zuckerberg ya kare Facebook kan zaben Trump

Asalin hoton, Getty Images
Mai kamfanin sada zumunta na Facebook Mark Zuckerberg ya kare shafin saboda zargin da aka yi masa cewa Facebook ne ya rika watsa labaran kanzon-kurege da suka bai wa Donald Trump nasarar zama shugaban Amurka.
Mr Zuckerberg, wanda ya yi jawabi a wurin wani taro kan fasaha da aka yi a California, ya ce bai kamata a dora wa Facebook alhakin cin zaben Trump ba.
A cewarsa, "Tunanin da wasu ke yi cewa Facebook ya watsa labaran kanzon-kuregen da suka yi tasiri a zaben kasar nan ba daidai ba ne."
Shugaban kamfanin na Facebook ya kara da cewa duk wanda ya amince cewa Facebook ya yi tasiri a zaben, bai fahimci irin sakonnin da magoya bayan Trump ke son isar wa a lokacin yakin neman zabe ba.
Wasu bayanai dai sun nuna cewa an rika watsa labaran karairayi wadanda suka bai wa Trump damar yin nasara fiye da labarai na gaskiya a shafin Facebook.
Mutane da dama, musamman Amurkawa, sun mayar da Facebook wani dandali da suka fi samun labarai.
























