Ana cin kasuwar Birrai

Bayanan bidiyo, Ana cin kasuwar Birrai
An wallafa

Wani bincike da BBC ta gudanar ta bankado yadda ake fasa kwaurin kananan birrai.

Wadannan dabbobin dai - ana kama su a dazuzzukan dake a yammacin Africa, akan kuma sayar da su ga masu bukatarsu a kasashen yankin Gulf da kuma China.

Binciken da aka gudanar daga gwamman kasashe - wani lokaci a bara, ya nuna cewa ana sayar da kowanne jaririn biri daya akan dala dubu goma- ($10,000).