Arhar kayan masarufi ka iya jefa tattalin arzikin duniya halin ka ka ni kayi — IMF

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Asusun lamuni na duniya, IMF, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin duniya ya ja da baya, sanadiyyar arhar kayayyakin masarufi da kuma rikice-rikicen siyasa.
A wani rahoto da aka saki a taron IMF da bankin duniya na shekara-shekara, asusun IMF, ya ce tattalin arzikin duniya bai kammala murmurewa ba, kuma a kasashe da dama bunkasar tattalin arzikin ba ta yi karfi ba.
Koda yake, asusun ya amince da cewar an samu karuwar hada-hadar harkokin tattalin arziki sanadiyyar karuwar zuba-jari da cinikayya da kuma samar da kayyayakin masana'antu, amma duk da haka ya yi gargadin cewa mutane da yawa a fadin duniya ba su ji wani sauyi a rayuwarsu ba.
























