An ware ranar tuna haihuwar Mugabe a matsayin hutu a Zimbabwe

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin Zimbabwe ta ayyana ranar tunawa da haihuwar hambararren shugaban kasar Robet Mugabe, a matsayin ranar hutu a ko wcace shekara, don nuna girmamawa gare shi na gudunmuwar da bayar wajen gina kasar.
Jaridar Herald ta kasar ta ruwaito cewa, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a ranar Juma'a bayan da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya sha rantsuwar kama mulki.
An dai ware ranar 21 ga watan Fabrairun ko wacce shekara ce a matsayin ranar hutu don girmama Mista Mugabe.
A watan Agustar da ya gabata ne gwamnatin Mista Mugabe ta yanke shawarar ware ranar tunawa da haihuwarsa a matsayin ranar hutu a kasar, sakamakon yawan kamun kafa da kungiyar matasa ta jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ta dinga yi.
A makon da ya gabata ne sojojin kasar da kuma jam'iyyarsa ta Zanu-PF suka tursasawa Mista Mugabe sauka daga mulki.

Tarihin rayuwar Robert Mugabe a takaice
- 1924: Shekarar da aka haife shi
- An horar da shi a matsayin malami
- 1964: Gwamnatin Rhodesia ta daure shi
- 1980: Ya lashe zaben da aka yi bayan 'yancin kai
- 1996: Ya auri Grace Marufu
- 2000: Bai yi nasara ba a zaben raba-gardamr da aka yi ba na karfin ikon shugaban kasa da kuma hana Turawa mallakar gonaki
- 2008: Ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da suka fafata da Tsvangirai, wanda ya janye saboda harin da aka kai kan magoya bayansa
- 2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin firai minista a lokacin da ake fuskantar durkushewar tattalin arziki a kasar
- 2016: An gabatar da takardun lamuni a yayin da karancin takardun kudya yi tsanani
- 2017: Ya kori mataimakinsa da ya dade suna aiki tare wato Emmerson Mnangagwa
























