Bale, Ozil, Neymar, Lukaku, Mourinho, de Ligt a kasuwar sayen 'yan wasa

Gareth Bale
Bayanan hoto, Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham a 2013
An wallafa

Tottenham za ta biya Real Madrid fan milyan £54 kan Gareth Bale mai shekara 30, sai dai ta ce ba za ta iya jure albashin dan wasan ba na fan miliyan £600,000 duk mako, a rahoton Express.

Arsenal za ta rasa damar daukar dan wasan Lyon kuma dan kasar Faransa mai shekara 25 Nabil Fekir, saboda ba ta son rabuwa da Mesut Ozil. (L'Equipe, via Sun).

Mesut Ozil

Shi kuwa tsohon dan wasan Arsenal Overmars wanda babban jami'i ne a kulob din Ajax, ya ce ya kamata Arsenal din ta maye gurbin Mesuz Ozil da Hakim Ziyech na Ajax mai shekara 26 dan kasar Morocco. (Calciomercato)

Kazalika, Goal ta ruwaito Overmars din yana cewa Juventus ta kusa kammala daukar kaftin din Ajax Matthijs de Ligt dan kasar Netherlands.

A gefe guda kuma, ita ma Barcelona ta fara shirin daukar dan wasan, in ji Mundo Deportivo.

Manchester United za ta mika tayin sayan dan wasan tsakiyar Sporting Lisbon Bruno Fernandes mai shekara 24 a cikin mako uku masu zuwa, in ji jaridar Independent.

Neymar ya shaida wa daraktan wasanni na PSG Leonardo cewa lallai yana son ya bar kungiyar a wata ganawa da suka yi. ESPN ta ruwaito.

Leicester City ta yi wa dan wasanta Harry Maguire mai shekara 26 alkawarin cewa zai iya tafiya idan har Man United ko Man City sun biya kudin da ya zarta wanda Liverpool ta biya kan Virgil van Dijk wato fan milyan £75. (Telegraph)

Jaridar Sun ta ce Newcastle za ta biya Sheffield Wednesday fansar fan miliyan £4 kan kocinta Steve Bruce da ta dauka.

Bayern Munich ta hakura da daukar Leroy Sane mai shekara 23 daga Man City kan kudi fan miliyan £100 a wannan karon, a rahoton Mail.

Mirror ta ruwaito cewa Victor Lindelof ya ce yana "matukar alfahari" da kasancewarsa dan wasan Man United duk da cewa wakilinsa ya ce Barcelona na nemansa.

Inter Milan tana dari-dari da farashin fan miliyan £75 da Man United ta saka wa Romelu Lukaku mai shekara 26. Yanzu dai tana neman a ba ta shi aro, inda za ta biya fan miliyan £9 da farko sannan ta cika £27 da kuma £27, in ji Star.

Tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho yana tunanin koma wa gasar Bundesliga a yunkurinsa na dawo wa harkar horarwa, in ji Independent.