Man Utd ta ba wa Roma Chris Smalling

Chris Smalling
Bayanan hoto, Chris Smalling ya ce ya ji dadin tafiya kungiya kamar Roma, ita ma ta ce ta ji dadin zuwan kwararre kamarsa
An wallafa

Dan wasan baya na Manchester United Chris Smalling ya tafi kungiyar Roma ta Serie A ta Italiya aro na kaka daya bayan da ta sayo wasu 'yan bayan da take ganin za su fi ma ta aiki.

Kungiyar ta Italiya za ta biya euro miliyan uku a zaman da dan wasan zai yi na shekara daya a can.

Smalling ya yi kaka tara a Old Trafford, inda ya dauki kofin Premier sau biyu, amma kuma ba ya daga cikin 'yan wasan da kociyan kungiyar na yanzu Ole Gunnar Solskjaer ke son amfani da su.

Dan bayan ya ji dadin tafiyar, yana mai cewa: ''Wannan wata kyakkyawar dama ce a gareni. Dama ce ta yin wasa a wata sabuwar gasa, a wata babbar kungiyar da ke da babban buri, abin da nake bukata kenan.''

Smalling da Luis Suarez
Bayanan hoto, Smalling ya fada wa Luis Suarez a wasansu na Zakarun Turai tsakanin Man Utd da Barcelona

Ita ma kungiyar ta Roma cewa ta yi ta tsinci dami a kala, inda darektanta na harkar wasanni Gianluca Petrachi, ya ce sun yi farin cikin dauko dan wasa kwararre kamar Chris.

Smalling, mai shekara 29 ya je United ne daga Fulham a 2010, kuma ya kara zamansa a Old Trafford zuwa shekara ta 2022 a watan Disamba.

Chris Smalling ya banke Messi
Bayanan hoto, Hancin Messi ya fashe a lokacin da Smalling ya far ma sa a haduwar da Barcelona ta doke United 1-0 a gasar Zakaru Turai

A kakar da ta gabata Smalling ya yi wa United wasa 34, amma sayen wani dan bayan dan Ingila Harry Maguire da United ta yi a kan fan miliyan 80, sai ya kasance ba ta damu da shi ba sosai.

Sannan kuma ga kari da dan wasan Sweden Victor Lindelof wanda ake ganin bayan za ta samu karfi sosai.

Sai dai kuma kociya Solskjaer ya ce Marcos Rojo, wanda ake cewa zai tafi AC Milan ko Marseille ko kuma Monaco, zai zauna daram tare da Phil Jones da Eric Bailly da kuma Axel Tuanzebe.