Manchester United na zawarcin Sancho

Asalin hoton, Getty Images
Mamallakin kungiyar kwallon kafar Leeds United Andrea Radrizzani ya bayyana cewa ya yi yunkurin dauko dan wasan Paris St-Germain da Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, da takwaransa dan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, wanda yake buga wasa a AC Milan, lokacin musayar 'yan wasa a Janairu. (Mail)
Manchester United na kan gaba wurin kokarin sayo dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund idan aka sake bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa a bazara. (Independent)
Real Madrid na fatan cewa idan ta bai wa Arsenal wani dan wasa da kuma karin kudi, za a ba ta dan wasan Gabon striker Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30. (Star)
Manchester United ta shirya sallama dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, wanda ta bai wa Roma aro, ga kungiyar, idan dai za ta samu damar sayo dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, 28. (La Gazzetta dello Sport, via Mail)
Arsenal ta yi yunkurin sayo Smalling a bazara inda Manchester United ta so sayar da shi a kan £25m. (Metro)
Dan wasan Tottenham da Belgium Jan Vertonghen, mai shekara 32, ya ce ba shi da tabbacin sabunta kwangilarsa a kungiyar a kakar wasa mai zuwa. (Mirror)
Arsenal na fatan za su cimma yarjejeniya da Real Madrid domin tsawaita zaman dan wasan Spain mai shekara 23 Dani Ceballo wanda ta karbo aro, idan kakar wasan bana ta wuce ranar 30 ga watan Yuni. (Standard)
Ana rade radin Leicester City za ta dauko dan wasan Atalanta da Belgium Timothy Castagne, mai shekara 24. (Sport Foot, via Leicester Mercury)
Kazalika ana hasashen Derby County za ta sayo dan wasan Fenerbahce Ferdi Kadioglu, mai shekara 20-year wanda ya wakilci Turkiyya a gasar 'yan kasa da shekaru 21. (Derby Telegraph)
Mai yiwuwa Arsenal ta dauko Dayot Upamecano daga RB Leipzig a yayin da ake hasashe cewa dan wasan mai shekara 21 zai bar kungiyar a bazara. (Bild, via Star)
West Brom na son sayo dan wasan Croatia Filip Krovinovic, mai shekara 24, a kwantaragir din-din-din idan ya kammala zaman aron da yake yi a Benfica. (Express and Star)
Za a iya tsawaita kasuwar musayar 'yan kwallon kafa ta bana zuwa watan Janairu a yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da dakatar da gasar Firimiya da ta EFL. (Express)
Tsohon dan wasan Arsenal da Tottenham Emmanuel Adebayor, mai shekara 36, ya makale a Benin saboda annobar coronavirus. Ya bar Paraguay, inda ya je domin halartar Olimpia da zummar ganawa da iyalinsa a Togo, amma yada zangon da ya yi a Benin ya sa dole ya killace kansa tsawon kwana 15. (Talksport)


























