Hakeem Otiki: An kori Janar na sojan Najeriya saboda cin hanci

Asalin hoton, Pr Nigeria
Wata kotun rundunar sojin Najeriya ta kama Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki, wanda zai yi ritaya baɗi, da laifuka biyar sannan ta bayar da umarni a rage masa mukami kana a kore shi daga aiki cikin wulakanci.
Otiki shi ne Kwamandan runduna ta 8 ta sojin Najeriya da ke Sokoto a watan Yulin July 2019 lokacin da ya aika sojoji biyar da ke aiki tare da shi su kai kudi daga Sokoto zuwa Abuja ta hanyar Kaduna amma kudin suka bata.
Kotun, wacce shugaban tsare-tsare na rundunar sojin, Laftanar Janar Lamidi Adeosun ya jagoranta, ta kama Otiki da laifin rashin biyayya ga dokokin soji, da satar kudin jama'a da karkatar da su da kuma shiga harkokin kasuwanci.
Kotun sojin ta yanke masa hukuncin da suka hada da: kora daga aiki a wulakance, rage masa mukami daga Manjo Janar zuwa Birgediya Janar da kuma jan kunnensa.
Kotu ta nemi ya koma da kudin da aka gano a wurinsa wadanda suka kai N135.8m da $6,600. Ta bukaci ya nemo N150m da bai fito da su ba sannan ya mayar cikin lalitar sojin kasar.
Za a zartar da wadannan hukunce-hukunce ne idan Majalisar Soji ta amince da su.
























