Ferran Torres: Watakila matashin ya bar Valencia ya koma Man City

Ferran Torres
Bayanan hoto, Ferran Torres ya buga wa Spaniya wasanni biyar a matakin matasa
An wallafa

Watakila dan kwallon Valencia, Ferran Torres zai iya kasancewa dan kwallo na farko da Manchester City za ta saya a matsayin wanda zai maye gurbin Leroy Sane.

Valencia na son fan miliyan 40 a kan Torres kuma BBC ta fahimci cewa dan kwallon Spaniyan mai shekaru 20 na son ya koma Etihad.

Dan kwallon Jamus, Sane ya bar City inda ya koma Bayern Munich.

City wacce ta kammala a matsayin kungiya ta biyu a kan tebur, na zawarcin dan wasan baya domin kara karfin tawagar a kakar wasa mai zuwa.

Dan kwallon Ingila, John Stones da kuma dan Argentina Nicolas Otamendi a yanzu babu tabbas ko za su samu dama sosai a kakar wasa mai zuwa - ganin cewa kungiyar tun bayan da aka dawo hutun korona, Guardiola ya fi amfani da Eric Garcia da kuma Aymeric Laporte.