Coronavirus a duniya: Manyan masu tunani na duba yadda duniya za ta kasance bayan annobar korona

Bayanan bidiyo, Yadda duniya za ta koma bayan cutar korona
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Akwai abu ɗaya da ake da tabbas a kansa kan wannan annoba da ake fama da ita a yanzu - za a samu manyan sauye-sauye. Amma muna da damar hasaso yadda sauye-sauyen za su kasance? Za mu iya tsara su?

Ko annonbar za ta ba da damarmakin kallon yadda duniya za ta zama nan gaba?

Tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙasar Costa Rica kuma fitacciyar masaniyar tattalin arziki ta duniya Rebeca Grynspan, ta ce duk da cewa a yanzu kusan dukkan ƙasashe na fuskantar matsin tattalin arziki a yanzu, ƙasashen da aka fi kira masu matsakaicin samu su ne za su fi jin jiki.

Ta yi kira ga ƙasashe cewa su haɗa kai su manta da bambance-bambancensu na siyasa da tattalin arziki don kare tare da tallafa wa ƙasashe marasa ƙarfi da mutum miliyan biyar da ke rayuwa cikinsu.

Shi kuwa Yuval Noah Harari masanin harkar tsaro kuma masanin tarihi sannan mawallafin littafin Sapien wanda aka sayar da kwafinsa miliyan 27, ya yi amannar cewa kayayyakin fasahar da ake ƙirƙira don yaƙar Covide-19 na iya zama silar samun tsarin kiwon lafiya mafi kyau da inganci a tarihi amma kuma zai iya zama wata hanya ta bin ƙwaƙƙwafi da leƙen asirin mutane na tsarin kama karya da ba a taba gani ba a duniya.