'Taron baza cutar Korona ne Fadar White House ta shirya'-Fauci

Dr Fauci
Bayanan hoto, Dr Fauci
An wallafa

Babban jami'in kwamitin yaki da annobar Korona a Amurka Dr Fauci ya ce Fadar White House ta yi gangancin hada bikin da ya yi sanadin barkewar annobar Korona.

Dr Fauci ya ce bikin da shugaba Trump ya hada da sunan gabatar da wadda yake so a kujerar alkali a kotun koli, ya zama wani bikin baza cutar.

Gomman ma'aikatan Fadar ne da kuma bakin da a ka gayyato su ka kamu da Korona bayan taron.

To sai dai jiya Juma'a ne likitan Mr Trump ya ce shugaban ya samu saukin da zai iya fita aiki cikin jama'a.

Tuni shugaban ya kira wani taro da zai karbi bakunci a Fadar White House din a yau Asabar.

Shugaba Donald Trump ya bar asibiti yana kuma ci gaba da samun sauki
Bayanan hoto, Shugaba Donald Trump ya bar asibiti yana kuma ci gaba da samun sauki

Da a ka tambayi shi game da bazuwar Korona a Fadar White House a hira da gidan talabijin na CBS, Dr Fauci ya ce 'alkaluman da mu ke gani a zahiri ba su bamu mamaki ba, lura da cewa an shirya bikin baza cutar Korona a Fadar White House'.

'Mutane sun cakudu wuri guda kuma bas a sanye da takunkumin rufe fuska.'

Dr Fauci ya kara da cewa 'tun watanni shida da suka wuce masana ke ta kira da a rika saka takunkumin rufe fuska', ya kuma yi watsi da maganar samar da Magana da Trump ke yi.

Har yanzu dokar hana hada manyan taruka na aiki a Washington, to amma ban da gine ginen gwamnati da su ka hada da Fadar White House.