Mamallakin Facebook, da WhatsApp da Instagram ya roki gafarar jama'ar duniya

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Wanda ya ƙirƙiro Facebook, Mark Zuckerberg, ya nemi gafara ga biliyoyin mutane a fadin duniya sakamakon katsewar shafukansa.WhatsApp, da Instagram da shi kansa Facebook sun daina aiki na awanni shida amma a yanzu sun dawo.
Lamarin ya hana mutane biliyan uku da rabi da ke amfani da shafukan damar shiga.
Masu sharhi na hasashen cewa matsalar da aka samu a jiya, na iya janyo wa kamfanin asarar da ta kai ta sama da dala miliyan 3, na harajin talluka a iya wannan taki.
Hannayen jarin Facebook sun rufe a kusan kashi biyar a New York.
Lamarin na faruwa ne kwana guda bayan wata mai bankada da ta taba aiki da kamfanin ta fallasa cewa Facebook ya fi fifita ribar da yake hankoron samu fiye da kare masu amfani da shafukansa.
























