An doke Andy Murray a Qatar Open

Murray
An wallafa

An doke Andy Murray a gasar cin kofin tennis ta Qatar Open.

Roberto Bautista ne ya fitar da dan kasar Burtaniyar a zagayen yan 16 da ci 6-0, da 6-1.

Andy Murray wanda ya taba zama gwarzon tennis na duniya ya taba lashe gasar ta Qatar Open a 2019.

Kuma tun a lokacin Andy Murray bai kara cin kofin daya-daya ba wato 'singles title'.

Amma kuma ya fara gasar ta Qatar Open da kafar dama, bayan da ya lallasa Taro Daneil dan kasar Japan.

Sai dai a yanzu Bautista Agut ya samu galaba kanshi, kuma shi ne zai kara da Davidovich Fokina wanda ya doke Dan Evans 4-6, 7-5, 6-4.