NBA: Stephen Curry ne dan wasa mafi kadari a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Stephen Curry ya kafa tarihi da cin maki 50 a wasan taurarin kwallon kwando na duniya ta NBA All-Star MVP a Cleveland.
An raba yan wasan zuwa tawaga biyu da sunan LeBron James da kuma Kevin Durant.
Curry mai shekaru 33 ya karya tarihin da Paul George ya kafa a 2016 na cin maki mafi yawa a irin wannan wasa.
Bayan kammala wasan an bai wa Stephen Curry kyautar kofin Kobe Bryant, a matsayin dan wasa mafi kadari a wasan taurarin kwallon kwando.
A yanzu an yi wa wasan na All-Star MVP suna na din-din-din, inda aka ska mata sunan Kobe Bryant.
Shahararren dan wasan na LA Lakers wanda ya sha lashe kyaututtuka a irin wannan wasa ya mutu shida 'yarsa Gianna, a wani hadarin jirgin helikwafta da aka yi a 2020 a Amurka.
Shima LeBron James maki daya ya hana ya kama tarihin tsohon dan wasan kwallon kwandon Kareem Abdul-Jabbar.
Dan wasan gaban Los Angeles Lakers din ne ya ci kwallon karshe a wasan na ranar Lahadi, kuma su suka yi nasara da maki 163 a Cleveland.




























