Europa League: Barca ta lallasa Napoli 4-2, Porto da Rangers sun tsallake

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta samu tsallakewa zagayen quarter-finals a gasar Zakarun Turai ta Europa, bayan da ta lallasa Napoli 4-2 har gida.
Tun kafin aje hutun rabin lokaci ne bakin suka ci kwallaye biyu ta hannun Jordi Alba da Frenkie De Jong.
Bayan nan Gerard Pique da Aubameyang suka tushe sauran a filin na Diego Maradona da ke Naples.
Masu masaukin bakin sun ci nasu kwallayen ne ta hannun Lorenzo Insigne da Matteo Politano, da hakan yasa aka tashi 4-2.
A Camp Nou kungiyoyin sun tashi 1-1, kuma tun a lokacin magoya bayan Barca suka ce suna da kwarin gwuiwar cewa kungiyar ta fara gano matsalolinta kuma ta fara magance su.
A sauran wasannin FC Porto ma ta tsallake bayan ta tashi 2-2 da Lazio a birnin Rome.
Dama Porto ta ci Lazio 2-1 a Focugal makon da ya wuce, kuma sakamakon na yau na nuna cewa ta tsallake da yawan kwallaye.

Asalin hoton, Getty Images
Hakama Real Betis ta fitar da Zenit St Petersburg ta Rasha bayan sun tashi babu ci.
A makon da ya wuce a birnin Saint Petersburg sun tashi 3-2, kuma dama ana hasashen da wahala a buga wasa a birnin na Rasha koda kungiyar ta fito saboda rikici.
Ita kuwa Rangers ta tashi 2-2- da Borussia Dortmund a Glasgow, to amma la'akari da cewa ta ci Dortmund 4-2 a Jamus hakan ya bata kai bantenta.
Yanzu za a jira a ga yadda hadin na quarter-finals zai kasance.
A wata mai kama da haka Arsenal ta doke Wolves 2-1, kuma a yanzu maki daya ya rage ta shiga cikin hudun farko a gasar Firimiya.
Dama wasan na daga cikin kwanton wasanni uku da Gunners ke da su, kuma idan ta kara cin wasa daya za ta sauko da Manchester United.



























