Ƙungiyoyin Saudiyya na neman Sancho, Madrid na sa ido kan Boniface

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaba na Barzil mai taka leda a Tottenham Richarlison, mai shekara 26, da dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 23, na daga cikin wadanda Saudiyya ke hakilon saya a watan Junairu mai zuwa. (Telegraph - subscription required)
Juventus na zawarcin Sancho, amma fa a matsayin bashi idan sun daidaita da United wadda za ta dinga biyan wani bangare na albashinsa. (Fabrizio Romano)
Har wa yau, United sun shirya domin sakar wa Sancho mara ya bar kungiyar da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan Junairu mai zuwa.(Football Insider)
Dan wasan baya na Ingila, Reece James, 23, ba zai taba barin kungiyar Chelsea da yake taka wa leda ba, duk da cewa Manchester City da Real Madrid na zawarcin sa kan jiki kan karfi. (90min)
Shugabannin kungiyar Manchester United, sun ki amincewa su gana da ejoji, idan har suna tunanin su na nenam wanda zai maye gurbin mana ja Erik ten Hag. (ESPN)
Dan wasan tsakiya na Brazil mai taka leda a Corinthia,Gabriel Moscardo, mai shekara 17, da ke daukar hankalin kungiyoyin Arsenal da Barcelona, ya ce kungiyar Chelsea na son daukar sa a kakar wasa mai zuwa. (Talksport)
Real Madrid sun kara sunan dan wasan tsakiya na Jamus Florian Wirtz, mai shekara 20, da mai tsaron gida na Netherlands,Jeremie Frimpong, dan shekara 22, da dan wasan gaba na Najeriya Victor Boniface, mai shekara 22, cikin wadanda suke fatan daukowa daga Bayern Leverkusen idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa. (Football Transfers)
Shugaban kungiyar Bayern Munich, Herbert Hainer ya tabbatar da cewa ba su da aniyar sayar da dan wasan baya na Canada Alphonso Davies, mai shekara 23, bayan an fara kwarmata rade-radin za a saida shi ga kungiyar Real Madrid. (90min)
Da alama dan wasan Croatia koma tsohon manajan Marseille,Igor Tudor, mai shekara 45, zai maye gurbin shugaban Napoli,Rudi Garcia, dan Faransa mai shekara 59. (Fabrizio Romano)
Shi ma Tsohon dan wasan baya na Italiya, Fabio Cannavaro, mai shekara 50, ka iya maye gurbin Garcia a kungiyar Napoli. (Mail)



























