Champions League ya dawo da ni Sevilla-Ramos

Sergio Ramos
An wallafa

Sergio Ramos ya ce gasar cin kofin zakarun Turai na da matukar muhimmanci a shawarar da ya yanke ta komawa ƙungiyar Sevilla a bana bayan kwantiraginsa da Paris St-Germain ta kare.

Dan wasan bayan, mai shekara 37, yana fatan murmurewa daga raunin da ya samu kafin Sevilla ta kara da Arsenal a Emirates ranar Laraba.

Ramos ya lashe gasar zakarun Turai sau hudu a kakar wasanni 16 da ya yi a Real Madrid.

Ramos ya ce "Sevilla na taka leda a gasar zakarun Turai kuma hakan ya yi tasiri wajen yanke wannan shawarar."

"Na sami tayin tafiya kasashen waje, kamar Saudiyya, misali - amma wannan bashi ne da na ci a kulob ɗina, Sevilla, kungiyar farko da na fara yin nasara."

Ramos bai buga karawar da suka tashi 1-1 a gasar La Liga da Celta Vigo ba a ranar Asabar, sai dai ya yi karin haske kan lafiyarsa kafin wasan da Sevilla za ta buga da Gunners a rukunin B.

"Karamin rauni ne. Ina fatan zan iya buga wasan amma ban sani ba ko wasan zai zo da wuri." In ji shi

Arsenal ce ke kan gaba a rukunin da maki shida yayin da Sevilla ke matsayi na uku, kuma tana neman nasarar farko a gasar ta bana.