Fifa ta nada alkalan wasan Najeriya da Mozambique

Super Eagles
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bayyana rafalin da za su busa wasan sada zumunta tsakanin Najeria da Mozambique da za su kara a Portugal.

Dan kasar Portugal, Miguel Nogueira shi ne zai busa wasan, yayin da Paulo Bras da Ana Loide da kuma Bruno Viera za su taimaka masa.

Wasan da za su buga a Estadio Municipal de Portimao ranar 16 ga watan Oktoba, shi ne na biyar da za su fuskanci juna a tsakaninsu a manyan wasanni.

A wasan sada zumunta da suka yi a Maputo, Super Eagles ce ta yi nasara da cin 1-0, daga nan suka yi karawa biyu a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a 2010

A can Maputo sun tashi canjaras, yayin da a Abuja a Oktoban 2009 Najeria ta yi nasara.

Da suka kara a gasar cin kofin Afirka a 2010 a Angola a 2010 fafatawar rukuni, Super Eagles ce ta yi nasara da cin 3-0 a birnin Lubango.

Super Eagles da Mozambique za su ƙara kece raini a Portugal ranar Litinin.

Tun daga ranar Talata 'yan wasan Super Eagles da aka gayyata suka fara halartar otal din Penin and Reasort, Portimao.

Tun kan wasan da Super Eagles za ta kara da Mozambique ranar Litinin za ta fara wasan sada zumunta da Saudi Arabia ranar Juma'a a dai Portugal din.