Chelsea ta hada maki uku a Goodison Park a wasan farko a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Everton ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Chelsea a wasan makon farko a gasar Premier League ta 2022/23 da suka fafata ranar Asabar.
Chelsea ta samu bugun fenariti daf da hutu, bayan da Ben Abdoulaye Doucoure yayiwa Ben Chilwell keta a da'ira ta 18 ta Everton.
Jorginho ne ya buga fenaritin, wanda ya kora golan Everton, Jordan Pickford gefe daya, sannan kwallon ta fada raga ta daya bangeren.
Chelsea wadda ta yi ta uku a bara da cin wasa 21 da canjaras 11 aka doke ta karawa shida, ta hada maki uku kenan a gidan Everton a farkon Premier ta bana.
Da wannan sakamakon Chelsea ta yi nasara karo na 20 a duk ranar fara babbar gasar tamula ta Ingia, Manchester City ce ke gabanta a wannan bajintar.
Sabbin fitattun 'yan wasan da Chelsea ta dauka a bana duk sun buga mata wasan a Goodison Park da suka hada da Raheem Sterling da Kalidou Koulibaly da kuma Marc Cucurella.
Everton karkashin Frank Lampard ta karkare a mataki na 16 a kasan teburin Premier da ta wuce, bayan cin wasa 11 da canjaras shida ta yi rashin nasara a wasa 21.
Wannan ita ce kaka ta 69 a jere da Everton ke buga Premier League tun daga 1954/55 - Arsenal ce kan gaba mai 97.



























