'Yan Real Madrid da za su kara da Napoli

Champions League
An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Napoli a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a Champions League ranar Laraba.

Cikin watan Oktoba, Real ta je Italiya ta doke Naoli 3-2 a wasa na bibiyu a rukuni na uku.

Sai dai Real Madrid tana fama da 'yan wasa da ke jinya da suka hada da Aurelien Tchouameni da Vinicius Junior da Eduardo Camavinga.

Da kyar ne idan Luka Modric zai yi wasan, wanda ya ji rauni a wasan da Real ta doke Cadiz 3-0 ranar Lahadi a La Liga.

Tuni koci Ancelotti ya sanar da 'yan wasan da zai fuskanci Napoli da su.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Fran and Cañizares.

Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger and Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Valverde, Ceballos, Mario Martín, Nico Paz and Theo.

Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim and Gonzalo.