Eto'o ya amsa cogen harajin fam miliyan 3.2 a Sifaniya

Samuel Eto'o
An wallafa

Tsohon dan kwallon tawagar Kamaru, Samuel Eto'o ya amsa laifin cogen harajin fam miliyan 3.2 a lokacin da yake taka leda a Barcelona.

An yanke wa gwarzon dan kwallon Afirka karo hudu hukuncin wata 22 na jeka gyara halinka, bayan da ya halarci zaman kotun a Sifaniya ranar Litinin.

Haka kuma zai biya kudin da ake binsa, da kuma tarar fam miliyan 1.55.

Masu shigar da kara a Sifaniya sun zargi Eto'o da kin bayyana kudaden shiga da aka yi tsakanin 2006 zuwa 2009.

Eto'o yana daga cikin jerin 'yan wasa da masu horar da tamaula da aka gabatar a gaban kotu kan cogen haraji a Sifaniya da suka hada da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Jose Mourinho da kuma Neymar.

Mai shekara 41, wanda shi ne shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru a yanzu haka, ya koma Barcelona a 2004 yana da shekara 23 a lokacin.

Ya kuma taka leda a Real Madrid da Inter Milan da Chelsea da kuma Everton, wanda ya yi ritaya a 2019.

Eto'o ya bayyana a kotun Ciudad de la Justicia da ke Barcelona tare da tsohon wanda ya kula da tamaularsa, Jose Maria Mesalles, wanda aka ci tara aka kuma yi masa daurin jeka gyara halinka na wata 12.