Nunez na fatan komawa kan ganiya karkashin Slot

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Liverpool, Darwin Nunez na fatan komawa kan ganiya karkashin sabon koci, Arne Slot, bayan da yake fuskantar kalubale a kakar nan.
Ɗan wasan tawagar Uruguay bai yi wani abin kirki ba da Liverpool ta ci Girona 1-0 ba ranar Talata a Champions League a Sifaniya.
Mohamed Salah ne ya ci ƙwallon a bugun fenariti, hakan ya sa Liverpool ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar zakarun Turai ta bana da maki 18.
Ƙwallo ɗaya ya zura a raga a wasa 10 baya, wanda ya ci uku jimilla tun fara kakar nan - bai kai yawan na Diogo Jota ba, wanda bai yi karawa 11 ba, sakamakon jinya.
Bayan da Jota ya fara buga wa Liverpool wasannin, sai Nunez mai shekara 25 ya koma zaman benci, har kuma ake sa Luis Diaz a madadinsa.
Daga nan magoya bayan Liverpool suka fara tantama kan ƙwazon ɗan wasan Uruguay, bayan da aka saye shi kan £85m a matakin mafi tsada a ƙungiyar.
Sabon koci, Arne Slot ya karɓi aikin horar da Liverpool da nufun bunkasa ƴan wasa, wanda kawo yanzu ya ci karawa 19 da canjaras ɗaya da rashin nasara daya a dukkan fafatawa 22 a bana.
Hakan ya sa Liverpool tana ta daya a kan teburin Premier da kuma a Champions League tana kuma buga FA Cup.
Nunez ya fara wasa 11 a kakar bana da takwas da ya canji ɗan wasa, sai dai ƙwallayen da ya ci a bana ba su kai yawan na bara ba guda bakwai.



























