Mainz za ta kori El Ghazi kan goyon bayan Falasɗinawa

Asalin hoton, Getty Images
Za a soke kwantiragin tsohon ɗan wasan Aston Villa da Everton Anwar El Ghazi a Mainz saboda wani saƙon da ya wallafa a dandalin sada zumunta game da rikicin Isra'ila da Gaza.
Kulob ɗin na Bundesliga ya dakatar da El Ghazi a ranar 17 ga Oktoba, bayan ya wallafa saƙon, wanda tuni aka goge.
A wata ganawar da suka yi a ranar Alhamis, kulob ɗin ya buƙaci ɗan wasan mai shekaru 28 ya nemi afuwa kan saƙon da ya wallafa da ya nuna cewa yana goyon bayan Falasdinawa.
Sai dai ɗan ƙasar Holland ɗin ya shaida wa manyan jami'an ƙungiyar cewa ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya yana kuma tare da duk waɗanda yaƙin ya shafa.
Majiyoyi sun shaida wa BBC ranar Juma'a cewa an sanar da El Ghazi cewa za a soke kwantiraginsa.
Ya mayar da martani inda ya wallafa a shafinsa na Instagram, yana mai cewa: “Na yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a ɓangaren Falasdinawa da Isra’ila.''
El Ghazi ya koma ƙungiyar ne a ranar 22 ga Satumba bayan ya bar PSV Eindhoven.























