Ina son ran dan wasa ya baci don ba a saka shi a wasa ba - Guardiola

Premier League
An wallafa

Pep Guardiola ya ce abu ne mai kyau idan 'yan wasansa na Manchester City za suke yin fushi, idan ba sa cikin 'yan sha dayan farko.

Jeremy Doku ya ci kwallo ya kuma bayar da hudu aka zura a raga a karawar da city ta caskara Bournemouth 6-1 ranar Asabar a Premier League.

Dan wasan yana benci a makon jiya a wasa da Manchester United, inda Jack Grealish ya buga fafatawar, amma sai aka yi sauyi a karawa da Bournemouth.

''Ina son Jack ya yi fushi, ina kuma son ya buga kwallo mai kyau,'' in ji Guardiola.

''Haka ma Doku - Ya ji haushin da bai buga wasa biyu baya ba. Wannan ce hanyar da za ta sa a dore a irin matakin nan.''

Manchester City ta koma ta daya a kan teburin Premier League ranar Asabar, yayin da Tottenham da Chelsea za su barje gumi a karashen wasan mako na 11.

Tottenham, wadda kawo yanzu ba a doke ta ba a kakar bana ba, bayan wasa 10, ita ce ta biyu, yayin da Chelsea mai maki 12 take ta ukun karshe.

Doku dan kwallon tawagar Belgium ya koma City kan fam miliyan 55 kan fara kakar bara, nan da nan ya sa kwazo a kungiyar da cin kwallo uku a dukkan karawa.

Mai shekara 21, yana buga gurbin da Jack Grealish ke yi, wanda ya yi zaman benci, amma ya shiga karawar daga baya a karshen mako.

Har yanzu dan kwallon tawagar Ingila, bai ci wa City kwallo ba a kakar nan, wanda ake fara wasa da shi cikin 'yan 11 din farko.

Gurdiola ya ce ''Idan har Jeremy da Jack za suke taka rawa mai kyau, zai iya saka su wasa tare. Amma idan ba sa kwazo a lokutan atisaye, za su iya saka kaimi da cewar akwai kalubale a gabansu.''