'Yadda ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar 'ya'yana uku'

ambaliyar ruwa
An wallafa

Yayin da damina ta kankama a Najeriya, kuma ake samun ruwan sama babu kakkautawa a wasu wuraren, wasu yankunan Jihar Jigawa na fuskantar matsalar ambaliya, wadda tayi sanadin asarar rayuka da muhallai.

A Unguwar Garko da ke garin Hadejiya, irin wannan ambaliyar ta yi sanadin rasa rayukan wasu yara uku bayan da soron gidansu ya rushe kuma ya danne su.

BBC ta ji daga mahaifinsu Mohammed Hassan, wanda ya bayyana yadda wannan lamari ya faru.

'' Ranar Lahadi da misalin karfe daya na dare, ana iska da ruwa wallahi soron ya fado yaran suna kwance, uku mata daya namiji.''

'' To kuma a ciki wadanda suka rasu biyu mata, daya namiji, daya kuma ta samu lafiya. Akwai yar shekara 10, da yar shekara bakwai sai mai shekara biyu da rabi, shine namijin, in ji mahaifin yaran.

Ya kara da cewa yanzu haka sun sake gida shida sauran iyalin nasa, kasancewar ambaliya ta rusa tsohon gidan nasu.

Malam Muhammad Hassan ya ce dama suna makwabtaka da wani tabki, kuma yana kyautata zaton cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi suka sa ya cika ya tumbatsa har ya yi sanadin afkuwar bala'in.

Sai dai ya ce daga lokacin zuwa jiya Litinin babu wani tallafi da ya samu daga gwamnati ko daidai ku, in banda aron matsuni da wani bawan Allah Ya bashi don zama da iyalinsa bayan rushewar gidansa.

Tuni aka yi jana'izar yaran uku a garin na Hadejiya, yayin da yar uwarsu da ta rayu ke ci gaba da murmurewa.