Arsenal da Liverpool sun shiga sahun masu neman Osimhen, Suarez na shirin hadewa da Messi

.
An wallafa

Liverpool ta bi sahun Chelsea da Arsenal wajen zawarcin dan wasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24, wanda aka kiyasta a kan fan miliyan 95. (Sun)

Dan wasan gaban Argentina Lionel Messi, mai shekara 36, ya yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa zai bar Inter Miami a matsayin aro don buga wa wata kungiya wasa da zarar an kare kakar wasannin MLS. (ESPN)

Inter Miami na fatan kawo dan wasan gaban Uruguay da Gremio Luis Suarez, mai shekara 36, zuwa kungiyar domin hada kai da tsohon abokin wasan Barcelona Messi. (Mirror)

Dan wasan bayan Chelsea dan kasar Brazil Thiago Silva, mai shekara 39, ya yi nuni da komawa Fluminense a shekara mai zuwa, inda kwantiraginsa da Blues zai kare a bazara. (Sun)

Bayern Munich na duba yiwuwar daukar matakin gaggawa kan tsohon dan wasan bayan Arsenal Sokratis Papastathopoulos, mai shekara 35, yayin da suke kokarin rage tasirin raunin ‘yan wasa. (Mirror)

Borussia Monchengladbach na Shirin tsawaita kwantiragin dan wasan tsakiyar Faransa Manu Kone a yayin da Liverpool da Juventus da kuma Bayern Munich ke zawarcin dan wasan mai shekaru 22. (90 Mint)

Newcastle na tunanin zawarcin dan wasan Bayer Leverkusen da Najeriya Victor Boniface, mai shekara 22. (Sun)

Bayern Munich na da kwarin gwiwar tsawaita kwanataragin dan wasan tsakiyarta na Jamus Jamal Musiala, wanda Liverpool da Manchester City ke zawarcinsa, yanzu haka kwantiragin dan wasan mai shekaru 20 zai kare a 2026. (90 Mint)

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta West Ham dan kasar Italiya Paolo di Canio, mai shekaru 55, ya bayyana kin amincewa da damar da ya samu ta shiga tawagar Roberto Mancini a matsayin kocin tawagar kasar Saudiya. (La Stampa)

Shahararren dan wasan Ingila Chris Waddle na iya yin rawar gani a wasan kwallon kafa mai shekaru 62 da haihuwa tare da kulob na biyu mafi tsufa a duniya. (Alan Biggs)