Faɗuwar Assad: Wasu shugabannin Gabas ta Tsakiya na ɗari-ɗari

Asalin hoton, AFP
Shugabannin kasashe daban-daban a yankin Gabas ta Tsakiya na bayyana matsayi da ra'ayoyinsu game da faduwar gwamnatin Bashar Al- Assad na Syria, wanda kungiyar 'yan tawayen HTS ta kora daga mulki a jiya Lahadi.
Yayin da wasu ke maraba da faduwar dadaddiyar gwamnatin ta Assad, tare da bayyana kwarin gwiwa na samar da makoma mai kyau ga kasar wasu kuwa na nuna fargaba da dari-dari ne.
A Iran ministan harkokin waje, Abbas Araghchi, wanda ya gaya wa kafofin yada labarai na kasar cewa Iran ka iya zama kawa ce ta Syria, to a mma tana gefe tana ganin abubuwan da ke faruwa.
Araghchi, ya ce ya yi mamakin yadda sojojin Syria suka kasa dakatar da 'yan tawayen.
Wasu shugabannin na yankin Gabas ta Tsakiyar kuwa wadanda a da suka yi maraba da Assad a cikinsu a yanzu suna zarginsa da saryar da damar gyara alakarsa da alummarsa ta Syria.
Wani jami'in gwamnatin Saudiyya ya ce lamarin sakamako ne na gazawar gwamnatin Syriyar ta sanya al'ummarta cikin harkokin siyasar kasar.
A kan martanin faduwar gwamnatin ta Assad, Amurka ta kasance kan gaba wajen bayyana ra'ayoyi na kasashen duniya, inda sakataren harkokin waje Anthony Blinken ya ce a karshe dai al'ummar Syria, sun samu dama ta makoma mai kyau.
Tun da farko Shugaba Biden ya bayyana faduwar gwamnatin da cewa ; cikakken adalci ne ga al'ummar Syria bayan shekaru aru-aru na danniya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yayin jawabin da ya gabatar na farko tun bayan faduwar gwamnatin ta Bashar al- Assad Shugaba Biden ya ce abubuwan da ke faruwa a kasar ta Syria, sun samar da yanayi na hadari da kuma rashin tabbas, to amma kuma wata dama ce mai tarihi ga kasar ta sama wa kanta makoma.
Biden ya yi alkawarin cewa Amurka za ta yi aiki tare da kawayenta kan hadarin da ke tattare da sauyin da aka samu tare da taimaka wa makwabtan kasar ta Syria.
Da yake magana a fadarsa ta White House Mista Biden ya bayyana hambarar da gwamnatin ta Assad a matsayin wani muhimmin abu na adalci;
Ya ce : ''A karshe dai gwamnatin Assad ta fadi . Wannan gwamnati ta gallaza tare da azabtarwa da kuma hallaka dubban 'yan Syria da ba su yi laifin komai ba. Faduwar gwamnatin babban abu ne na adalci. Lokaci ne mai dama ta tarihi ga al'ummar Syria da suka dade cikin akuba su gina makoma mai kyau ga kasarsu abar alfahari.''
Shi kuwa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ta'allaka faduwar gwamnatin ta Assad ne ga matakan da ya ce Isra'ila ta dauka a kan abokan Shugaba Assad din ne - Hezbollah da Iran.
A lokacin da ya kai ziyara Tuddan Golan da ke kan iyakar Isra'ila da Syria, Netanyahu ya ce ya umarci dakarunsa da su kame yankunan da a da suke tudun-mun-tsira domin hana mayakan da ke gaba da kasarsa amfani da wajen.




























