Southgate ya gayyaci Harry Maguire tawagar Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Ingila Gareth Southgate ya gayyaci tsohon kyaftin din Manchester united Harry Maguire tawagar Ingila don fafatawa a wasannin da za ta buga da Australia da kuma Italiya a watan Oktoba a filin wasan Wembley.
Wasa ɗaya ne tal aka fara da Maguire a United a kakar wasan bana inda ya buga wasan gasar Carabao cup da suka doke Crystal Palace da ci 3-0 a ranar 26 ga Satumba.
Kocin na ingila ya kuma sake kiran dan wasan Aston Villa Ollie Watkins wanda ya buga wa Ingila wasan karshe a watan Maris na 2022.
Amma dan wasan gaban Chelsea Raheem Sterling bai sami shiga cikin jerin 'yan wasan kasar ba a karo na hudu a jere.
Jarrod Bowen na West Ham, wanda aka kira zuwa tawagar Ingila a karon farko a watan Mayun 2022, ya dawo bayan ya rasa gurbi a tawagar a watan Satumba.
Har ila yau an gayyaci dan wasan gaban Arsenal Bukayo Saka, duk da cewa dan wasan na fama da raunin da ya tilasta masa fita daga wasan Arsenal da Lens bayan mintuna 34 ranar Talata.
Ingila za ta kara da Australia a wasan sada zumunci a ranar 13 ga watan Oktoba kafin ta fafata da Italiya a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2024 a ranar 17 ga Oktoba.
Tawagar ƴan wasan Ingila
Masu tsaron gida : Sam Johnstone, Jordan Pickford, Aaron Ramsdale.
'Yan wasan baya: Levi Colwill, Lewis Dunk, Marc Guehi, Harry Maguire, John Stones, Fikayo Tomori, Kieran Trippier, Kyle Walker, Trent Alexander-Arnold.
'Yan tsakiya: Jude Bellingham, Conor Gallagher, Jordan Henderson, Kalvin Phillips, Declan Rice.
'Yan wasan gaba: Jarrod Bowen, Phil Foden, Jack Grealish, Harry Kane, James Maddison, Eddie Nketiah, Marcus Rashford, Bukayo Saka, Ollie Watkins.



























