Dole a nuna jin-ƙai a rikicin Isra'ila da Falasɗinu - Mo Salah

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Liverpool dan kasar Masar Mohamed Salah ya yi kira ga shugannin duniya da su hada kai wuri guda domin kare ci gaba da kashe rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba a yakin da ake yi tsakanin Israila da Falasdinawa.
Jami'an lafiya sun ce abin fashewa da ya tashi a wani asibiti a birnin Gaza ya kashe ɗaruruwan mutane a daren ranar Talata.
Dan wasan mai shekara 31 ya ce dole ne a bari a shiga da kayan agaji Gaza cikin gaggawa.
Salah ya ce "abubuwa masu tayar da hankali sun faru tun bayan ɓarkewar rikicin".
Jami'an Falasdinawa sun zargi Isra'ila da kai harin da ya kashe mutane a asibitin al_Ahli.
Sai dai ita ma Isra'ila ta ce masu ikirarin jihadi na Falasdinawa ne suka kai harin bisa kuskure, ta kuma musanta zargin da aka yi mata.
Salah ya ce abin da ya faru a asibitin abin tashin hankali ne.
Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce "mutanen Gaza na bukatar abinci da ruwa da magani cikin gaggawa".
"An kassara rayuwa, an raba iyalai da ƴan'uwansu, dole a dakatar da wannan kisan kiyashi."



























