Yadda Falasɗinawa ke laluben 'yan uwansu a gine-ginen da harin Isra'ila ya ruguza

Asalin hoton, Reuters
Mutane sun yi dogon layuka domin karban fetur a zirrin Gaza, yayinda aka shiga kwana na biyu ta yarjejeniyar tsagaita wutar wucin gadin kwanaki hudu da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas.
'Yan Gaza na amfani da wannan dama ta tsagaita wutar wucin-gadi domin tattara duk wani abu da suke bukata, da neman 'yan uwa da abokan arziki, sannan akwai masu tattaki domin shakar iskar 'yanci a bakin teku.
Wasu sun ziyarci gidajensu – ko akwai abin da ya rage musu – domin ganin asarar da suka yi da kuma 'yan abubuwan da za su iya tsinta.
Wannan yarjejeniya ta bada damar kara adadin abubuwan bukatar agaji da ake kai wa a yankin na Falasɗinawa.
Isra'ila ta datse damar shiga Gaza bayan kaddamar da hare-haren ramako da zummar kakaɓe kungiyar Hamas, bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da suka zargi mayaƙan da kashe musu mutum 1,200 a kudancin Isra'ila da kuma garkuwa da sama da 240.
Tun bayan wancan lokacin, sama da Falasɗinawa 14,500 aka kashe a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas.
Yarjejiniyar ta kwanaki huɗu, da Qatar ke shiga tsakani, ta kunshi sakin 'yan Isra'ila 50 da kuma Falasɗinawa 150 da ake rike da su a gidajen yarin Isra'ila.
A rana ta farko ta soma aikin yarjejeniyar, kusan motoci 150 ne suka shigar da kayan agaji Gaza daga Masar.
Yayin da wannan ke kasance adadi mafi yawa na agaji da ake shigarwa Gaza tun bayan ratsa iyaka da ayarin motocin agaji suka yi a ranar 21 ga watan Oktoba, Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai bukatar ƙarin agajin.
An kaste kusan layukan sadarwa da samun bayanai a sassan Gaza, amma hotunan da ake wallafawa daga zirrin na nuna yadda mutane suka yi dogayen layuka domin karbar fetur da sauran bukatun agaji a Rafah, da ke kudancin yankin.

Asalin hoton, reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Motoci sun jeru suna dakon izini shiga Gaza ta iyakar Rafah da ke Masar, ɗauke da kayan abinci da ruwa da fetur da magunguna.
Sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa tankokin mai huɗu da kuma na iskar gas huɗu sun shiga Gaza a safiyar ranar Asabar.
Yanayi ne mai tafiyar hawainiya tsallake iyakar da ayarin motoci, saboda binciken da sojojin Isra'ila ke yi kafin su amince a ƙetare.
Kungiyar agaji Red Cross ta Falasɗinawa tace manyan motoci 61 ɗauke da kayan abinci, da Ruwan sha da magunguna sun taso daga Rafah kuma sun kuma doshi arewacin Gaza.
Ta ce wannan zai kasance ayari mafi girma da ke isa arewacin yankin tun soma wannan yaƙin.
Gwamnatin Isra'ila ta ce tana sa ran manyan motocin agaji 226 su shiga yankin ta iyakar Nitzana da ke kudancin Isra'ila.
"Wannan ya haɗa da motocin abinci 113, bakwai na magunguna, sai 27 na Ruwan sha, 43 kuma na kayayyakin amfanin gida ko matsugunai, sai motoci 25 na kayayyakin gyaran jiki da tsafta," a cewar Eytan Schwartz kakakin gwamnati.
Akwai kuma ƙarin motoci 11 na Masar da ke dauke da kayayyakin lafiya da za a kai asibitin Emirati, a cewarsa.

Asalin hoton, reuters
Duk da farin cikin da mutane da dama ke nunawa kan tsagaita wutar, ana bayyana mabambanta ra'ayoyi na baƙin ciki da farin ciki bayan da dama sun dawo sun iske gidajensu da muhallai a ruguje, domin tsintar abin ɗauka da kuma jana'izar gawawwakin 'yan uwa da iyalai da ke binne a ɓaraguzan gine-gine.
Tahani al-Najjar ta yi amfani da wannan dama wajen dawo wa gidanta da aka ruguza a Khan Younis a ranar Asabar, a cewar kamfanin dilanci labarai na Reuters.
Matar mai shekara 58 a duniya ta yi kokarin kwashe wasu kofunan roba a ɓaraguzan gidanta, da take cewa sojojin Isra'ila sun lalatasu a hare-haren sama tare da kashe mutum bakwai daga cikin iyalan gidanta.
A kudancin birnin wasu mutanen na zaune a tantuna a wajen asibitin Nasser yayinda suke dako da nazari komawa yankinsu na arewacin zirrin.
Ana iya ganin kwandunan tumatir, da lemu da albasa da sauran kayan marmari da na gwari a titunan kasuwar birnin.
Mai Magana da yawun hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Juliette Touma, ta shaidawa BBC cewa ana cikin yanayi na tsanani, kuma duk da cewa kayayyakin agaji na shigowa Gaza a yanzu akwai bukatar kari.
Ta ce akwai bukatar kayayyakin tsafta da magunguna da fetur da abinci.
Akwai mutanen da dama da bayan suturar jikinsu basu da komai, kuma galibinsu ko wanki ba sa yi.
Sansanonin agajin da aka ware ya cika ya batse, a cewarta, makarantu da cibiyoyinsu na ɗauke da sama da mutane miliyan guda da wannan yaƙi ya ɗaiɗaita.




























