Bowen ya yi burus da manyan Premier, Juventus na son aron Sancho

Asalin hoton, GETTY
Ɗan wasan gaba na Ingila Jarrod Bowen, wanda ake dangantawa da tafiya Liverpool da Newcastle United ya amince da ƙulla sabon kwantiragi a West Ham. (Fabrizio Romano)
Watakila Juventus ta ɗauki aron Jadon Sancho, na Ingila a watan Janairu kafin ta saye shi gaba-ɗaya a bazara mai zuwa. (Sun)
Jose Mourinho ya ce hankalinsa na kan aikinsa na horarwa a Roma, amma kuma ya ce ba ya fid da tsammanin cewa wata rana nan gaba zai yi aiki a Saudiyya. (MBC Egypt daga Reuters)
Roma ta ƙaryata rahotannin da ke cewa za ta kori Mourinho domin maye gurbinsa da tsohon kocin Jamus Hansi Flick idan ta yi rashin nasara a gidan Cagliari a wasansu na Lahadi. (ANSA daga Football Italia)
Napoli na duba yuwuwar maye gurbin Victor Osimhen, wanda kwantiraginsa zai ƙare a 2025, da Gabriel Jesus, na Arsenal ko Alvaro Morata na Atletico Madrid ko kuma ɗan wasan Lille da tawagar Kanada Jonathan David. (Calciomercato)
Manchester City da Real Madrid za su fafata wajen zawarcin matashin dan wasan bayan Kanada Alphonso Davies, mai shekara 22, wanda kuma ke iya wasa a gefen gaba, saboda kwantiraginsa zai ƙare da Bayern Munich a 2025 (Fichajes)
Brighton ba za ta amince da sharaɗin bayar da damar sayar da ɗan wasan gaba na gefe na Japan ba Karou Mitoma, wanda rahotanni ke cewa ƙungiyoyin Premier da dama na sonshi, a sabon kwantiraginsa. (Football Insider)
Manchester United za ta tsawaita kwantiragin ɗan bayanta na Sweden Victor Lindelof ta yadda zai ci gaba da zama har watan Yuni na 2025. (Star)
Chelsea na sha'awar sayen matashin ɗan wasan gaba na Belgium Lois Openda, mai shekara 23, daga RB Leipzig ta Jamus. (Football Transfers)
Sabon kwantiragin shekara biyar na ɗan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimarae a Newcastle ya ƙunshi damar sayar da shi a kan fam miliyan 100.(Guardian)
Wakilin matashin ɗan bayan Bayer Leverkusen da Ecuador ya ce, Liverpool na daga cikin ƙungiyoyin da ke son Piero Hincapie, mai shekara 21. (90 min)
Atletico Madrid ta sanya wa Barcelona farashin yuro miliyan 80 idan tana son riƙe matashin ɗan wasanta na gaba na Portugal Joao Felix, mai shekara 23, da ta karɓa aro. (AS )
Tottenham na sa ido a kan ɗan wasan gaba na gefe na Galatasaray daTurkiyya Kerem Akturkoglu. (Fotospor daga Goal)
Wasu bayanai na nuna cewa Sheffield Wednesday na tattaunawa da tsohonɗan Bayern Munich kuma mataimakin koci Danny Rohl, mai shekara 34, domin zama sabon kocin ƙungiyar bayan korar Xisco Munoz. (Sheffield Star)



























