'Yan Kenya da 'yar wasan Najeriya a hotunan Afirka na mako

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga Afirka ko kuma 'yan nahiyar na wannan makon.

An ɗauki hoton wani mutum yana tsaka da tsinkar fiya a wata gona da ke yankin Al Qalyubia na ƙasar Masar ranar Laraba
Bayanan hoto, An ɗauki hoton wani mutum yana tsaka da tsinkar fiya a wata gona da ke yankin Al Qalyubia na ƙasar Masar ranar Laraba
A gonar dai, wata mata tana nuna cikin ɗan itaciyar
Bayanan hoto, A gonar dai, wata mata tana nuna cikin ɗan itaciyar
Wannan matar kuma ta yi tsayuwar ɗaukar hoto bayan ta kaɗa ƙuri'arta a Kajiado da ke kudancin Kenya a zaɓen shugaban ƙasar na ranar Talata...
Bayanan hoto, Wannan matar kuma ta yi tsayuwar ɗaukar hoto bayan ta kaɗa ƙuri'arta a Kajiado da ke kudancin Kenya a zaɓen shugaban ƙasar na ranar Talata...
...Jimawa kaɗan, bayan kaɗa ƙuri'a sai aka fara ƙirga ƙuri'un a Ɗakin Taro na Mathare Social da ke Nairobi babban birnin ƙasar lokacin da sararin samaniya ya yi dishi-dishi
Bayanan hoto, ...Jimawa kaɗan, bayan kaɗa ƙuri'a sai aka fara ƙirga ƙuri'un a Ɗakin Taro na Mathare Social da ke Nairobi babban birnin ƙasar lokacin da sararin samaniya ya yi dishi-dishi
A ranar Laraba, wani mutum ke nan ake gani ɗauke da akwatin zaɓe yana isa ofishin hukumar zaɓe a Nairobi.
Bayanan hoto, A ranar Laraba, wani mutum ke nan ake gani ɗauke da akwatin zaɓe yana isa ofishin hukumar zaɓe a Nairobi.
A birnin Birmingham na Birtaniya ranar Lahadi, 'yar wasan Najeriya Ruth Usoro na yin duk abin da za ta iya a wasan tsallen baɗake a gasar Wasannin Ƙasashe Rainon Ingila.
Bayanan hoto, A birnin Birmingham na Birtaniya ranar Lahadi, 'yar wasan Najeriya Ruth Usoro na yin duk abin da za ta iya a wasan tsallen baɗake a gasar Wasannin Ƙasashe Rainon Ingila.
A Ireland kuma, gomman 'yan Kenya ne suka taru don kallon wani mutum ne ke yin alkafira yayin da Kenya da Jamaica ke shirin fafatawa a gasar wasanni ta Lacrosse ranar Laraba
Bayanan hoto, A Ireland kuma, gomman 'yan Kenya ne suka taru don kallon wani mutum ne ke yin alkafira yayin da Kenya da Jamaica ke shirin fafatawa a gasar wasanni ta Lacrosse ranar Laraba
...A ranar Larabar dai, an sha dariya da nishaɗi a Bikin Edinburgh da aka yi a Scotland
Bayanan hoto, ...A ranar Larabar dai, an sha dariya da nishaɗi a Bikin Edinburgh da aka yi a Scotland
An ci gaba da shagali lokacin da matan suka fara waƙa
Bayanan hoto, An ci gaba da shagali lokacin da matan suka fara waƙa
A kusa da yankin Mbombela kuwa na Afirka ta Kudu a ranar Asabar, bishiyoyin lemo ne ke girma.
Bayanan hoto, A kusa da yankin Mbombela kuwa na Afirka ta Kudu a ranar Asabar, bishiyoyin lemo ne ke girma.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da takwararsa ta Afirka ta Kudu Naledi Pandor ne ke haɗa gwiwar hannu bayan ya sauka a Pretoria don ganawa yayin ziyararsa a ƙasashen Afirka ranar Litinin.
Bayanan hoto, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da takwararsa ta Afirka ta Kudu Naledi Pandor ne ke haɗa gwiwar hannu bayan ya sauka a Pretoria don ganawa yayin ziyararsa a ƙasashen Afirka ranar Litinin.
Mutane ne ke tsaye a cikin ruwan ambaliya a birnin Dakar na Senegal ranar Juma'a
Bayanan hoto, Mutane ne ke tsaye a cikin ruwan ambaliya a birnin Dakar na Senegal ranar Juma'a
Idan muka koma Kenya kuma a ranar Alhamis, wani ɗan acaɓa ne ya lulluɓe jikinsa da tutar ƙasar yayin da suke jiran sakamakon zaɓen na ranar Talata
Bayanan hoto, Idan muka koma Kenya kuma a ranar Alhamis, wani ɗan acaɓa ne ya lulluɓe jikinsa da tutar ƙasar yayin da suke jiran sakamakon zaɓen na ranar Talata
An kuma samu walwali a Switzerland ranar Laraba, inda mawaƙiya 'yar Birtaniya da Eritrea Lula Merabrahtu ta fito kan jan kafet a bikin fim na Locarno karo na 75.
Bayanan hoto, An kuma samu walwali a Switzerland ranar Laraba, inda mawaƙiya 'yar Birtaniya da Eritrea Lula Merabrahtu ta fito kan jan kafet a bikin fim na Locarno karo na 75.

Dukkan hotunan da masu su