Wolves ta sayar wa Al Hilal Ruben Neves fam miliyan 47

Ruben Neves
Bayanan hoto, Neves ya ci kwallo 30 a wasa 253 a dukkan karawar da ya yi wa Wolves.
An wallafa

Wolverhampton ta amince da tayin fam miliyan 47, domin sayar da kyaftin ɗinta Ruben Neves ga Al Hilal ta Saudi Arabia.

Mai shekara 26 ɗan kasar Portuguese mai taka leda daga tsakiya, yana da sauran yarjejeniyar kaka daya da Wolves.

Bayan kammala kakar da ta wuce Neves ya yi kwadayin komawa Barcelona, wadda ta yi shirin zawarcin dan kwallon.

To sai dai kungiyar Barcelona ba ta yi wani tayin da zai nuna tana son daukar Neves ba, wanda ya yanke shawarar komawa buga gasar Saudi Arabia.

A watan nan Karim Benzema ya kammala komawa Al Ittihad, yayin da ake alaƙanta N'Golo Kante da bin sawunsa.

Tun cikin Disamba Cristiano Ronaldo ya amince da komwa kungiyar Al Nassr, bayan da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Manchester United.

Wannan cinikin ya faranta ran Wolves, wadda take neman kuɗin da za ta bai wa koci, Julen Lopetegui domin ya karo 'yan wasa don fuskantar kaka mai zuwa.

Neves yana tare da Wolves tun daga 2017 da aka sayo shi daga Porto.

Ya taimaka kungiyar ta lashe Championship da komawa buga Premier League da kaka biyu da ta dunga karwa a mataki na bakwai.

Kungiyar ta je gasar Europa League, wadda ta kai quarter finals a 2020, inda Sevilla ta fitar da ita.

Daga lokacin kokarin kungiyar ya dinga yin kasa, wadda ta karkare a mataki na 13 a teburin Premier League da aka kammala.