James Maddison ya fice daga tawagar Ingila saboda rauni

James Maddison
An wallafa

James Maddison ya fice daga tawagar Ingila a wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2024 a watan Nuwamba saboda rauni a idon sawunsa.

Ɗan wasan tsakiyar mai shekaru 26 ya samu raunin ne a fafatawar da Tottenham ta sha kashi a hannun Chelsea da ci 4-1 a gasar Premier ranar Litinin.

Ingila za ta kara da Malta a Wembley ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba kafin ta tafi Arewacin Macedonia kwanaki uku bayan haka.

Tottenham ta ce Maddison "zai ci gaba da zama a Hotspur Way don murmurewa tare da ma'aikatan lafiya na kulob ɗin".

Ƙungiyar ba ta bayyana tsawon lokacin da take tsammanin ɗan wasan zai yi jinya ba.

Maddison ya zura kwallaye uku kuma ya taimaka an ci biyar a wasanni 11 na gasar Premier da ya buga wa Spurs tun lokacin da ya koma ƙungiyar kan farashin fam miliyan 40 daga Leicester City a watan Yuni.

Ya buga wa Ingila wasanni biyar kuma ya kasance wanda ba a yi amfani da shi ba a wasan da suka doke Italiya da ci 3-1 a watan Oktoba wanda ya tabbatar da cancantar shiga gasar Euro 2024 ga tawagar Gareth Southgate.

Tottenham wanda ke matsayi na biyu a teburin Premier za ta ziyarci Wolves ranar Asabar