An ci Arsenal karo na biyu a Premier kawo yanzu

Declan Rice
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Newcastle United ta yi nasara a kan Arsenal da cin 1-0 a wasan mako na 10 a Premier League ranar Asabar.

A minti na 12 da fara wasa ne Newcastle ta zura ƙwallo a raga ta hannun Alexander Isak a karawar da suka yi a St James Park.

Arsenal wadda ta fara wasan da kwarin gwiwa ta yi kokarin farke ƙwallon, amma hakan bai samu ba daga wajen Newcastle.

Da wannan sakamakon Newcastle ta yi sama zuwa mataki na takwas a teburi, yayin da Arsenal ta ci gaba da zama a matakinta na uku.

Gunners, wadda ta buga karawa 10 kawo yanzu, ta yi nasara biyar da canjaras uku aka doke ta fafatawa biyu da fara kakar nan.

Wasan da aka buga a Premier League a bara tsakanin Newcastle da Arsenal:

Premier League Asabar 24 ga watan Fabrairu 2024

  • Arsenal 4 - 1 Newcastle

Premier League Asbar 4 ga watan Nuwamba 2023

  • Newcastle 1 - 0 Arsenal

Kenan Arsenal ta yi wasa uku a jere a Premier League, amma ta samu ɗaya, shi ne wanda ta tashi 2-2 da Liverpool, kafin nan ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Bournemourth.

Wasannin da ke gaban Arsenal:

Champions League Laraba 6 ga watan Nuwamba 2024

  • Inter da Arsenal

Premier League Lahadi 10 ga watan Nuwamba 2024

  • Chelsea da Arsenal

Premier League Asabar 23 ga watan Nuwamba 2024

  • Arsenal da Nottm Forest