Kounde ba zai buga wa Barcelona El Clasico ba

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Barcelona, Jules Kounde da kyar idan zai buga wasan El Clasico kamar yadda kungiyar ta sanar.
An sauya Kounde a karawar da Barcelona ta tashi 2-2 a gidan Granada a La Liga ranar Lahadi, bayan da ya yi karo da abokin wasansa Gavi.
Rahotannin na cewar Kounde zai yi jinyar wata daya ko fiye da hakan, wanda zai bi sahun Robert Lewandowski da Frenkie de Jong da Pedri da kuma Raphinha da ke jinya a kungiyar.
Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid ranar 28 ga watan Oktoba a La Liga, wasan hamayya daga cikin karawar da Kounde ba zai yiwa kungiyar Camp Nou ba.
Kafin nan Barcelona za ta fuskanci Athletic Bilbao ranar 22 ga watan Oktoba da kuma wasan Champions League da Shakhtar Donetsk ranar 25 ga watan Oktoba.
Mai tsaron bayan ya buga wa Barcelona fafatawa 11 a dukkan karawa da fara kakar bana, inda Barcelona take mataki na uku a teburin La Liga.
Haka kuma Kounde ba zai yi tawagar Faransa wasan neman shiga gasar nahiyar Turai ba da za ta kece raini ranar Juma'a da wasan sada zumunta da Scotland ranar Talata.
Wani dan wasan da ke jinya da ba za su buga wa Faransa wasannin ba ya hada da William Saliba na Arsenal, wanda aka maye gurbinsa da Jean-Clair Todibo.



























