Chelsea na bibiyar Liam Delap, Liverpool da Arsenal na gogayya kan Martin Zubimendi

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta karkatar da akalarta zuwa ga zawarcin ɗan wasan gaban Ipswich da Ingila mai shekara 21, Liam Delap, bayan ta janye daga zawarcin ɗan wasan gaban Newcastle da Sweden mai shekara 25, Alexander Isak. (The I - subscription required)
Arsenal na fatan ɗaukar Isak a cikin watan Janairu, inda take sa ran kwaɗaita masa buga gasar zakarun Turai domin shawo kansa zuwa Emirates. (GiveMeSport)
Ɗan wasan gaban Faransa, Christopher Nkunku ba ya jin dadɗin zaman sa a Chelsea saboda rashin samun damar buga wasa, amma har yanzu ɗan wasan mai shekara 27 bai fara tunanin barin Stamford Bridge ba. (Athletic - subscription required)
Liverpool ta shirya sake ƙaddamar da zawarcin ɗan wasan tsakiyar Real Sociedad mai shekara 25, Martin Zubimendi a watan Janairu, amma tana fuskantar ƙalubale daga Arsenal wadda itama ke sha'awar ɗaukar ɗan wasan Sifaniyan. (Teamtalk)
Newcastle na bibiyar ɗan wasan gaban Lyon da Faransa mai shekara 21, Rayan Cherki da kuma ɗan wasan Lille da Canada mai shekara 24, Jonathan David yayin da take neman ɗan wasan gaban da za ta ɗauka a watan Janairu. (The I - subscription required)
Ɗan wasan gaban jamhuriyar Ireland mai shekara 20, Evan Ferguson, n afatan barin Brighton 20 a watan Janairu saboda ƙarancin samun damar taka leda a ƙungiyar.(Football Insider)
Tottenham na fatan shiga gaban Manchester United da Newcastle wajen sayen ɗan wasan tsakiyar Lille da Ingila mai shekara 24, Angel Gomes. (GiveMeSport)
Ɗan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 17, Lamine Yamal, ya ƙulla yarjejeniyar fatar-baka da za ta sa ya tsawaita kwangilarsa da Barcelona zuwa nan da shekara shida, amma ba zai sanya hannu a yarjejeniyar ba har sai ya cika shekara 18 da haihuwa a watan Yulin badi. (El Chiringuito TV, via Football Espana)
Manchester City ta karkata akalata ga zawarcin ɗan wasan tsakiyar Sporting da Uruguay mai shekara 24, Maximiliano Araujo. (Football Insider)
Newcastle na kan gaba a jerin masu sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Algeria mai shekara 18, Ibrahim Maza, bayan Hertha Berlin ta sauke farashi a kan ɗan wasan zuwa £16.65m. (Caught Offside)






























