Me ya sa Elon Musk ke harba dubban tauraron ɗan adam sama?

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin SpaceX mallakar Elon Musk yana ta harba dubban taurarin bil adama zuwa subahana. Mutane da yawa sun ce sun ga taurarin a samaniya.
Suna cikin wani aikin kamfanin Starlink, wanda ya ke nufin samar da intanet mai udu daga sararin subahana zuwa lunguna masu wuyar zuwa a duk fadin duniya.
Mene ne Starlink kuma yaya yake aiki?
Starlink na samar da yanar gizo ne ta hanyar amfani da taurarin dan adam masu alaqa da juna.
Suna da nufin isa ga mutanen dake zaune a karkara da kauyuka inda ba a iya samun intanet mais auri.
“Akwai mutane a UK a cikin wannan rukuni, amma sun fi yawa a rogowar duniya, a wurare kamar Africa,” a cewar Dr. Lucinda King, mai lura da sashen Space Projects da ke jami’ar Portsmouth. A ajje taurarin Starlink a mafi kasa na sararin subahana kuma suka yi kusa da duniyar mu, domin tabbatar da sadarwa mai sauri tsakanin taurarin da kuma kasa cikin hanzari.
Sai dai akwai taurarin dan adam masu yawa dake kusa da duniya da ake bukata domn samar da yanar gizo a duk fadin duniya. Ana tunanin Starlink ya harba wasu taurari 3000 zuwa sararin subahana tun shekara ta 2018. Ana kyautata zaton zai bukaci taurari 10,000 ko 12,000 a cewar Chris Hall.
“Amfani da taurari zai warware matsalar rashin samun intanet a kebabbun wurare dake hamada da tsaunuka,” a cewar shi.
“Zai zagaye bukatar gina manyan na’urori dake amfani da kebura da karafunan samar da network domin isa wadannan yankunan.”
Mene ne farashin Starlink kuma waye zai yi amfani da shi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan aka kwatanta da intanet din da kamfanonin gargajiya suke samarwa, Starlink bashi da saukin farashi.
Ana biyan $99 a wata (£89 a wata a Birtaniya). Faifan dish da na’urar dake kamo intanet din daga tauraro na kamawa $549 (£529 a UK).
Amma 96% na gidaje a Birtaniya na da intanet mai gudu, haka zalika 90% a Tarayyar Turai da Amurka.
”Mafi yawancin kasashen da suka cigaba da duk duniya suna da intanet mai kyau,” a cewar Farfesa Sa’id Mosteshar, Darektan Manazartar Manufofi da Dokokin Sararin Subahana a Jami’ar London. ”Sun dogara akan ‘yan kananan kasuwanni domin samun kudaden shiga.”
Kamfanin ya ce yana da kwastomomi 400,000 a kasashe 36 da yake haskawa – mafi yawacin su a nahiyar Amurka ta Arewa, Turai da Australasia. Wannan ya kunshi gidaje da masana’antu.
A shekara mai zuwa, Starlink na shirin fadada intanet din shi zuwa gidaje a Africa da nahiyar Amurka ta Kudu zuwa Asia – yankunan duniya inda babu intanet sosai.
”Farashin Starlink zai iya yin tsada ga gidaje da yawa a Afirka” a cewar Chris Hall. ”Amma zai iya taka rawa mai muhimmanci wajen kusantar da makarantu da asibitoci a yankunan karkara a can.”
Ta ya Starlink yake taimako a Ukraine?
Yayin da dakarun Rasha ke cigaba da kutsa kai cikin Ukraine, sun dakatar da sadarwar intanet kuma suna yunkurin toshe shafukan sadarwa.
Elon Musk ya baiwa Ukraine intanet din Starlink ana fara yakin na Ukraine. An tura faifan dish misalin 15,000 zuwa kasar.
”Har yanzu Starlink na aiki, kamar ma’aikatar gwamnati,” inji Chris Hall. ”Har yanzu Rasha ba ta samu yadda zata hana shi aiki ba”.
An yi amfani da shi fagen daga.
“Dakarun Ukraine na amfani da shi wajen sadarwa – misali, tsakanin shedkwata da sojoji a filin fama,“ a cewar Dr Marina Miron, wani manazarcin harkokin yaki dake Jami’ar Kins a London. „“Baza a iya toshe internet din ba kamar radiyon gargajia, kuma yana daukar mintuna 15 wajen hadawa ya fara aiki.“
Ko Starlink na cika sararin subahana da tarkace?
Ba Starlink kadai ba, akwai abokan gasa kamar OneWeb da Viasat – wadanda su ma suke samar da intanet daga sararin subahana kuma suna aika dubban taurarin dan adam zuwa samaniya.
Wannan zai jawo matsala a cewar Sa’id Mostehar.
”Zai kara yiwuwar hadari a sararin samaniya musamman inda taurari za su ringa karo,” a cewar shi.
”Taurarin dan adam zasu iya karo da wasu na’urorin kuma hakan zai samar da baraguzai da ka iya yin barna mai yawa idan suna tashi da gudu.”
A baya an samu lokuta da taurarin Starlink su ka kusa yin karo har da tashar sararin subahana na mallakar kasar Sin.
“Idan akwai baraguzai da yawa, hakan zai kara yiwuwar hadari a lokuta masu zuwa a bangaren sararin samaniya da ake ajje taurarin dan adam,” a cewar Dr Kina na Jami’ar Portsmouth.
“Kuma zai iya yiwuwa ba za mu iya ficewa daga bangaren sararin subahana na kasa-kasa zuwa wani sabon bangare da yafi sama, wajen da taurarin dan adam masu samar da hana da wayar tarho suke ajje.”
Taurarin Starlink suna kuma janyo matsaloli a manazarta taurari.
A lokacin fitowar rana da faduwar ta, za’a iya ganin su da ido saboda rana na haska fukafukin su. Wannan zai jawo hasken da ba a bukata a kan na’urar leken taurari, lamarin da zai hana ganin wasu taurarin da duniyoyin.
”Manazarta taurari sun ga matsalar da wuri,” a cewar Farfesa Mosteshar. “Su ne na farko da suka yi korafi.”




























