Bayern Munich ba ta bukatar Ronaldo, Zinchenko ya zama dan Arsenal

Oleksandr Zinchenko
Bayanan hoto, Oleksandr Zinchenko
An wallafa

Daraktan wasanni na Bayern Munich Hasan Salihamidzic ya sake nanata cewa kungiyarsa ba ta da sha'awar dauko Cristiano Ronaldo dan wasan gaba mai shekara 37 daga Manchester United. (SPORT1 via Mail on Sunday)

Manchester City ba su da niyyar sayar da Bernardo Silva, dan wasanta na tsakiya mai shekara 27 ga Barcelona a wannan sabuwar kakar wasan, inda koci Pep Guardiola ke son amfani da shi sosai. (Sunday Mirror)

Arsenal ta amince da wani tayi na fam miliyan 30 da Manchester City ta yi ma ta kan Oleksandr Zinchenko, dan wasan baya dan kasar Ukraine mai shekara 25. (Fabrizio Romano)

Chelsea kuwa za ta yi yunkurin dauko Jules Kounde, dan wasan baya na Sevilla mai shekara 23 kuma dan Faransa ne bayan da ta kasa samun Nathan Ake mai shekara 27 dan Manchester City. (Times - subscription required)

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya shaida wa shugabannin kungiyarsa cewa ya kamata su ci gaba da kokarin dauko Frenkie de Jong, dan wasan tsakiya mai shekara 25 daga Barcelona. (Guardian)

Barcelona ta bayyana De Jong cikin 'yan wasan da za ta tafi Amurka da su domin wasannin shirin sabuwar kaka mai zuwa. (Manchester Evening News)

Everton ta fara tattaunawa da Anthony Gordon, dan wasan gaba dan kasar Ingila mai shekara 21, bayan da ta ki amincewa da wani tayi na fam miliyan 35 da Newcastle United ta mika ma ta kan dan wasan. (Football Insider)

AC Milan na tattaunawa da Tottenham kan dauke Japhet Tanganga, dan wasanta na baya mai shekara 23. (Calciomercato in Italian)

Paris St-Germain ta bi sahun Barcelona a kokarin sayo Carney Chukwuemaka dan wasan tsakiya mai shekara 18 daga Aston Villa. (Sunday People)

Juventus kuwa na ganawa da Atletico Madrid kan dauko Alvaro Morata, dan wasan gaba mai shekara 29 kuma dan kasar Sfaniya, wanda ya koma kungiyar bayan ya shafe kakar wasa biyu a kungiyar ta Italiya a matsayin dan aro. (Calciomercato - in Italian)

Nottingham Forest ta yi wa Middlesbrough tayin fam miliyan 10 domin raba ta da Marcus Tavernier, dan wasan gefe mai shekara 23. Bournemouth ma ta bayyana sha'awar saye dan wasan dan kasar Ingila. (Mail on Sunday)

Dan wasan baya na Manchester United Phil Jones mai shekara 30 na cikin 'yan wasan da sabon kocin DC United Wayne Rooney ke hankoron saya. Jones da Rooney sun taba buga wasa tare a Old Trafford. (Daily Star Sunday)