Har yanzu NFF ba ta biya Super Falcons ba
Wafcon 2022: Me yasa NFF ta gaza biyan Super Falcons kudadensu?

Asalin hoton, backpage
Tun bayan kammala gasar cin kofin Afrika ta mata a Morroco, har yanzu Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ba ta biya tawagar yan matan ba, wato Super Falcons.
Hakan na zuwa duk da bajintar da tawagar ta nuna ta kaiwa zagayen kusa da na karshe, inda mai masaukin baki wato Morocco ta yi waje da ita.
Kazalika tawagar ta ci kofunan na gasar Wafcon sau uku a jere kafin Afrika ta Kudu ta taka mata burki a Morocco.
Kuma ta lashe kofin na nahiyar Afrika sau tara jimilla.
Dama a lokacin da ake tsakiyar gasar yan matan sun kaurace wa yin atisaye gabanin wasansu da Zambia a zagayen kasashe Quarter-finals.
Ko wacce daga yan wasan na biyar NFF dala 10,000, da suka hada da ladan cin wasanni uku kafin Morocco ta cire su a zagayen kusa da karshe.
Wasu daga cikin yan wasan sun fada wa BBC cewa suna fargabar cewa ba za a biya su ba kwata-kwata tunda har aka kammala gasar aka dawo gida.
To amma a hira da BBC, Janar Sakatare na Hukumar ta NFF Dr Muhammad Sanusi ya ce ko wane lokaci daga yanzu za a iya biyansu, duk da ba zai iya fadin takamaimai ranar da hakan zata faru ba.
'' Ni kaina na zauna da su na fada musu cewa muna fuskantar wasu kalubala, bamu son kafin mu biya su su yi abunda zai bata ma kasarmu suna''.
''Kasan yadda harkar kudi yadda take amma ana nan ana kokarin a biya su in Allah ya so,'' in ji Dr Sanusi.
Ya kara da cewa sun biya su wani kaso na kudin tuntuni, abunda ya rage kudaden ladan lashe wasannin da suka yi a gasar Wafcon 2022 da wasu wasanni daya ko biyu kafin gasar.
Ba wannan ne karon farko ba da tawagar yan matan Super Falcons suka yi bore bayan kasa biyansu kudaden alawus din gasussukan da suke wakiltar Najeriya.





























