An dakatar da Mourinho da cin shi tara saboda caccakar rafli

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da Jose Mourinho wasa ɗaya da cin shi tarar £15,000, sakamakon caccakar alkalan wasa a karawar da Fenerbahce ta doke Trabzonspor.
Tsohon kociyan Chelsea da Manchester United ya shiga fili a guje da faɗuwa kasa da gwiwa biyu, bayan da Sofyan Amrabat ya ci ƙwallo na uku daf a tashi.
To sai dai kociyan ya soki alkalan wasan babbar gasar tamaula ta Turkiya kan yadda suke gabatar da aikin su.
Hukumar ƙwallon kafar Turkiya ta ce kalama da Mourinho ya yi, ba su kamata kuma sun saɓa ka'ida.
Ta kara da cewar tsohon wanda ya horar da Real Madrid da Inter Milan ya yi furucin da zai ɓa ta kwazon alkalan da sauran jami'ai kan batun son rai da rashin adalci.
Wasan da ya ci karo da takaddama, Mourinho bai ji dadin da aka bai wa mai masaukin baƙi Trabzonspor fenariti biyu ba - dukkansu sai da aka tuntubi VAR, wadda ta fayyace abinda ya faru.
Ya kuma ce su kan su ya kamata a basu bugun fenariti tun kan su ci ƙwallo na uku ta hannun Amrabat.























