'Yan wasan Nigeria Super Eagles sun isa Cameroon

'Yan wasan Najeriya
Bayanan hoto, Super Eagles sun taka rawar gani sosai a karawar farko ranar Juma'a
An wallafa

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun isa birnin Yaounde gabanin sake karawarsu da Kamaru ranar Litinin a wasan share fagen zuwa gasar cin Kofin Duniya wacce za a yi badi a Rasha.

A ranar Juma'a ne kasashen biyu suka yi fafatawar farko a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a Najeriya, inda Kamaru ta yi rashin nasara da ci 4-0.

Najeriya ce kan gaba a rukunin B, inda take da maki tara.

Zambia ce ke biye mata da maki hudu sai Kamaru mai maki biyu.

Aljeriya ce kurar baya inda ta ke da maki daya kacal bayan wasa uku.

'Yan wasan Super Eagles na fatan sake samun nasara a wasan na ranar Litinin domin sake karfafa matsayinsu a saman teburin rukunin na B.

Kasar da ta zo ta daya ce kawai za ta samu damar zuwa gasar ta duniya, wacce Rasha za ta karbi bakunci a badi.

Otel din da 'yan wasan Super Eagles suka sauka a birnin Yaounde
Bayanan hoto, Otel din da 'yan wasan Super Eagles suka sauka a birnin Yaounde