Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

An wallafa

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

Hauwan Daushe
Bayanan hoto, Wani mai wasa da wuta lokacin da ake Hawan Daushe a birnin Zariya ranar Lahadi
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da yake kallon wasan Kamaru da Najeriya a talabijin wanda aka tashi kunnen doki (1-1) ranar Litinin
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mai dakinsa Aisha
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mai dakinsa Aisha yayin da suka isa Abuja ranar Laraba, bayan kammala hutun babbar sallah a Daura jihar Katsina
Mataimakin shugaban Najeriya a jihar Benue
Bayanan hoto, Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo tare da Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yayin da Mista Osinbajo ya kai ziyara jihar ranar Laraba don jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
sabon Ofishin 'yan sanda a jihar Nasarawa
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Nasarawa Umar Tanko Al-Makura tare Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, yayin bikin kaddamar da hedkwatar rundunar 'yan sanda a garin Lafia na jihar Nasarawa ranar Alhamis
Ginin hedkwatar rundunar 'yan sanda a garin Lafia wanda gwamnan jihar ya ba rundunar kyauta ranar Alhamis
Bayanan hoto, Ginin hedkwatar rundunar 'yan sanda a garin Lafia wanda gwamnan jihar ya ba rundunar kyauta ranar Alhamis
Shara
Bayanan hoto, Wata hanyar ruwa da aka cika da shara a unguwar Nyanya da ke jihar Nasarawa ranar Lahadi