Bakar fata sun fi wahala a 'yan ci-ranin zuwa Turai

Asalin hoton, AFP
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaran da suka fito daga kasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara, sun fi dandana kudarsu a tsakanin 'yan ci-rani ko 'yan gudun hijira da ke kokarin shiga Turai daga Libya da Turkiyya.
A wani bincike kan ci-rani da Asusun tallafa wa yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF, tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar suka yi, sun gano cewa matasa daga kasashen, da suke bi ta Libya don shiga Turai, su ne suka fi shiga hadarin gallazawa da wariya.
Wadanda suka gudanar da binciken tare da hada rahoton sun ce bambancin launin fata ne ma ya fi jefa su cikin wannan akuba.
Binciken ya nuna cewa rukunin wadanda suka fi shan wuya ko gamuwa da wahalhalun da ke tattare da tafiyar, kamar yadda aka yi tsammani su ne matasa ko yara 'yan shekara 14 zuwa 17.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan karancin shekarun hadari da wahalar sun ma fi tsanani ga wadanda ba su da ilimi.
Karin wuyar kuma shi ne idan aka ce su kadai suke tafiyar, sannan a ce sun fito ne daga kasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara, to a nan kuma wahala sai iya wadda suka gani, domin kusan a ce ba ta da iyaka.
Duka wadannan bambance-bambance na daga cikin abubuwan da masu gallaza musu ke la'akari da su wajen mutunta su ko wahalar da su.
A gaba dayan wannan tafiya ta ci-rani ko hijira zuwa kasashen Turai daga Afirka, wadanda suke bi ta Libya sun fi yarinta a kan masu jarraba sa'arsu ta hanyar gabashin tekun Bahar Rum, wato hanyar da ta bi ta Turkiyya.
Masu rahoton suka ce yawan safarar mutane da yadda ake mayar da su kamar 'yan sarka da sanya su aikin tilas, duka sun fi tsanani a bangaren Libya.

Asalin hoton, Others
Baya ga cewa tafiyar ta fi nisa da hadari, akwai maganar nuna wariyar launin fata da kyama da ake nuna wa masu bi ta Libya su shiga Italiya fiye da wadanda suke bi ta Turkiyya.
'Yan ci-rani da dama da aka tattauna da su sun ce, an ware su daga cikin takwarorinsu a wannan tafiya aka gallaza musu saboda kawai su bakake ne.



























