Hotunan yadda 'yan Afirka ke wahalar samun abinci

A cow passes in front of the backdrop whilst a shoot takes place.
An wallafa

A kudu da hamadar Saharar Afrika, rikici da sauyin yanayi sun yi tasiri a kan kiyaye abinci. Al'ummomi a Nijar da Burundi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka suna fuskantar mummunan hadari na yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Chris de Bode ya ziyarci wuraren, ya tafi da da niyyar daukar hotuna wadanda zai iya amfani da su a wani shirin talabijin mai nuna hotuna.

Tare da binciko yadda tasirin siyasa da muhalli zai iya rage kwarin gwiwar mutane su noma abincin da za su ci, de Bode ya kuma nuna yadda ayyukan jin kai za su taimaka.

A young man holds up his tools.

Daniel Nsabiyaremye dan shekara 28, ya koyi aikin kafinta ne amma sai dai ba shi da kayan aiki. Bayan jerin basussukan da ya karba don sayen kayan aiki kamar su guduma da kusosi da sauransu, a karshe ya samu damar fadada sana'arsa da a yanzu take samun tagomashi.

Ya ce: ''Na sayi kayan ne daya bayan daya, daga kudaden da na ranto wadanda ake turo min ta banki."

''Yanzu, ina da hanyar wadata iyalina da abinci. Kafin wannan shirin, sau daya muke cin abinci, kuma abincin ba mai inganci ba ne. Amma yanzu sau biyu muke cin abinci. Hakan ya yi tasiri matuka wajen iganta lkafiyata da ta iyalina."

Two men stand in front of a backdrop.
A group sit in front of a backdrop.

Joseph da Nyambaronziza mambobi ne a al'ummar Batwa da ake tauye wa hakki. An san mutanen al'ummar Batwa da gajarta.

Dukkansu suna fadi-tashin ciyar da iyalansu, wadanda suke rayuwa a gidajen da suka zama kamar kufai a yankin Kabere da ke cikin kungurmin da ji kusa da duwatsu a kasar Uganda.

Suna samun kudi daga kananan ayyukan lebaranci da aikin gona ko kuma neman daham a cikin wani rafi da ke kusa.

A woman picks plants.
A bowl of beans
A family stand next to their house.

Denise Nyamwiza 'yar shekara 20, tana kula da kannanta ne bayan da iyayensu suka mutu shekara biyu da suka wuce sakamakon cutar maleriya.

Ta kan nemi aiki a wasu lokutan kuma tana sayar da fiya da wasu kayan lambun da take nomawa a 'yar karamar gonarta.

Solange Wanibilo na tsaye ita da iyalanta a kofar gidansu a kauyen Bomandoro, da ke Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka. Dan autan Solange, Arthur da jikanta Frank suna fama da tamowa.

A family stand in front of their house.
A small boy's arm is measured.
A woman stands with her four children.

Golden Marlenue tana tsaye da ya'yanta guda hudu.

'Yan kananan yaran sune Naomi 'yar shekara biyu da kuma Athanase 'yar shekara daya wadanda duk suke fama da tamowa. Amma mako uku da suka wuce aka sake bude asibitin sha-ka-tafi na Ndanga, wanda a baya aka rufe shi, kuma yanzu yara suna iya samun kulawa da magungunan da su ke bukata.

Light streams into a woman's house.
A plant pushes through the soil.
A group sit in a field.

A Boganando da ke Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka, Josephine Zawele tana ta tsaye a wata gona ta wata makaranta tare da sauran mambobin al'ummar.

Wannan gonar manoma suna amfani da ita ne don koyan sababbin hanyoyin aikin gona da za su iya amfani da su a gonarsu.

Hadijatou Cheihou, 'yar shekara 15, na zaune ne a kauyen Gao Moussa da ke Jamhuriyyar Nijar, wanda suka yi suna sosai a samar da man gyada. Hadijatou ta na daya daga cikin mambobin kungiyar mata 30 da aka ba su horo don samar da man gyada.

Yanzu mata fiye da 90 a kauyen suna samun horo. Mutane na yin tafiyar kilomita fiye da 45 don su sayi man.

A woman stands in her village.
Legs of a family.
A woman smiles out from a group.

A kauyen Kosama da ke Jamhuriyyar Nijar, Hassana Abdourahamane na murmushi tare da wasu mambobin al'ummar manoma.

Suna noma kayan lambu a gonar da aka ba su aro, kamar su albasa da tumatir da dankali da karas da kabeji da sauran su. Wata kugiya mai suna Concern, ita ta dauki nauyin ba su horo da samar musu da iri, amma yanzu matan sun fara dogaro da kansu saboda sun sayar da amfanin gonar da suka girbe.

A bundle of vegetables.
A farmer holds a child.
A farmer stands amongst his animals.

A da, Salifou Ahment, manomi mai shekara 70, na fadi-tashin ciyar da dabbobin da ya ke kiwatawa a lokacin rani.

Yanzu maimakon yin doguwar tafiya don sayen abinci, akwai wata bankin sayar da abincin dabbobi a kusa da gidansa. Bankin, wanda al'umma ke tafiyar da shi, na ajiye abincin dabbobi a ko wanne lokaci na shekara, kuma yana sayar wa da manoma a farashi mai rahuwa.

A dusty cup.

Ana iya kallon hotunan a harabar St Martin da ke dandalin Trafalgar a Landan daga ranar 19 ga watan Satumba.