Me ya sa maza ke nuna son kai wajen samun mukamai?

Bayanan bidiyo, Me ya sa maza ke danne mata wajen samun mukamai?
An wallafa

Maza na ci gaba da fin mata yawa a samun manyan mukamai a duniya.

Bincike ya gano cewa ko a shugabancin kamfanoni ma mata ba su da yawa.

To ko mata na kai wa gaci a cimma muhimman mukamai kuwa, ko kuwa dai suna cin karo ne da matsaloli a kokarin kai wa ga hakan?