IS ta fitar da sakon murya na al-Baghdadi

al-Baghdadi bai kara fitowa bayyanar jama'a an ganshi ba
Bayanan hoto, Tun bayan watan Yulin shekarar 2014, al-Baghdadi bai kara fitowa bainar jama'a ba
An wallafa

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta IS, ta wallafa wani sautin murya da aka nada wanda ta ce na shugabanta ne, Abu Bakr al-Baghdadi.

Sakon da mai maganar ke yi a cikin sautin, ga alama yana yi ne a kan barazanar da Koriya ta Arewa ke yi wa Japan da kuma Amurka.

Kazalika sautin muryar ya tabo batun yakin da ake yi a babbar tungar kungiyar ta IS da ke birnin Mosul, birnin da dakarun Iraqi suka karbe a watan Yulin da ya gabata.

Al-Baghdadi, wanda aka sanya ladan dala miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da labarin in da yake, ba a kara ganinsa a bayyanar jama'a ba tun watan Yulin shekarar 2014, lamarin da ya janyo rade-radin cewa ko yana raye ko kuma ya mutu.

Karshen ganinsa da aka yi a baynar jama'a shi ne, lokacin da ya yi wa'azi a babban masallacin birnin Mosul wato al-Nuri, bayan IS din ta karbe ikon birnin.

Ko da aka tambayi kakakin rundunar sojin Amurka da ke yaki da IS, Ryan Dillon, ya ce tunda babu wata kwakkwarar shaida da za mu ce ya mutu, to za mu dauka yana nan da rai.