Me zai faru idan Amurka ta fara yaki da Koriya ta Arewa?
An wallafa
Wadansu masana harkokin tsaron Amurka da Koriya ta Arewa sun yi wa BBC karin bayani game da abin da zai faru a makonnin farko na fara yaki tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.
"Kimanin mutum miliyan biyu za su rasa rayukansu a makonni farko na fara yaki tsakanin kasashen biyu - wadanda duka sun mallaki makamin kare dangi," kamar yadda tsohon sojan Amurka, David Maxwell ya yi hasashe.
Har ila yau, masanin ya ce yakin zai jawo a tafka mummunar asara tsakanin kasashen biyu musamman idan Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi amfani da makamin Nukiliyarsa.