An daba wa wadansu mata biyu wuka a Faransa

Asalin hoton, Reuters
An caka wa wadansu mata biyu wuka har ta kai ga ajalinsu a tashar jirgin kasa ta birnin Marseille a Faransa, a wani al'amari da ake zaton harin ta'addanci ne.
Jami'an tsaron da ke aiki a tashar sun harbi maharin, wanda dan kimanin shekara 30 ne.
Har ila yau 'yan sanda sun bayyana cewa ya yi kama da mutanen da suka fito daga yankin arewacin Afirka.
Wadanda suk shaida al'amarin sun ce sai da "maharin ya yi kabbara da karfi" kafin ya aikata hakan.
Kungiyar da ke ikirarin kafa Daular Musulunci [IS] ta ce maharin, daya daga cikin sojojinta ne.
Maharin ya yanki daya da cikin wadanda harin ya rutsa da su ne a wuya, dayar kuma ya caka mata wuka a ciki.
'Yan matan wadanda harin ya rutsa da su 'yan shekara 17 da kuma 20.
Shugaban Faransa Emmauel Marcon ya bayyana harin da "aikin ta'addanci" wanda abin kyama ne.
Har ila yau ya yi gode wa sojoji da 'yan sanda wadanda suka ba da gudummawa a lokacin harin.
Harin ya faru ne kusa da wani banki a wajen tashar jirgin kasa ta Saint Charles a yankin kudancin Faransa.
Ministan harkokin cikin gidan kasar, Gérard Collomb, ya fada wa manema labarai cewa maharin ya gudu ne bayan da ya kai hari na farko, amma sai ya dawo don ya kara kai wani hari.



























