Hotunan wadanda gobara ta kona a gobarar Ghana

An wallafa

Ku kalli wasu hotunan wadanda suka kone sakamakon gobarar da ta afku Ghana ranar Lahadi. Akwai hotuna masu ta da hankali.

Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Kawo yanzu an kai mutum arba`in da suka samu raunuka asibiti, amma biyu daga cikinsu sun mutu.
Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Zuwa yanzu akwai mutum 12 da suka samu mummunan rauni suke kuma cikin firgici inda aka kai su bangare na musamman don kula da su.
Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Mutum biyu da suka ji mummunan rauni kuma suna bangaren kula da cutar da ta yi tsanani.
Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Hukumomi sun ce yawan gobara da ake samu a baya-bayan nan na da alaka da sakaci.
Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Wasu kuma sun karye a hannu, wasu a kafa, wasu a kafada saboda lokacin da abin ya faru sun dimauce suna ta guje-gujen ceton rai.
Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Sun danganta hakan da sakaci da rashin bin ka`idojin sauke iskar gas daga bangaren masu kula da cibiyoyon siyar da iskar gas, da deribobin motocin daukar iskar gas din da kuma yaran motarsu.
Marasa lafiya na gobarar Ghana
Bayanan hoto, Wani babban jami'i ya ce: "Idan aka duba lokacin da irin wannan gobara ta fi abkuwa shi ne lokacin da ake sauke iskar gas, kuma kafin a sauke iskar gas akwai matakai da ka`idoji da suka kamata a dauka don kaucewa irin wannan bala'i.